Post by Muhammad Auwal Umar on Mar 29, 2014 5:16:08 GMT
172. TAMBAYA : – Wai gaskiya ne, wanda aka sanya a wuta ba zai fita ba har abada?
Wai domin a cikin Alkur’ani, tun daga Bakara har Nasi, inda Allah y ace “Wuta zai ce ‘Khalidina Fiha Abaddan”?
AMSA : – Eh, “Khalidina Fiha” shi suka fiya yawa, amma akwai wadanda za a sa su a ciki sai sun gasu, sannan a fitar da su. Watau dai in mutum ya shiga (wutar), amma yana da Imani, yana fita wanda yake akwai’ Mis Kala Zarratin, na Imani a cikin zuciyarsa in ya shiga wuta, zai fita.
Kuma Allah (SWT) yana fidda shi saboda ceton Annabi (S.A.W).
173.
TAMBAYA : – A wane wuri ne a cikin Alkur’ani idan aka nuna cewar idan kafuri ya mutu; ya mutu ke nanhar abada?
AMSA : – A’a ba a cewa ya mutu har abada ba, cewa aka yi “LA YA MUTU FIHA, WALA YAHAYAH (Suratul A’LAH).
Watau in kafuri ya shiga wuta, ba zai mutu ba balle ya huta.
Sannan kuma ba zai rayu ba balle ya ji dadi.
174.
TAMBAYA : – Ina hukucin mai yi wa sabon musulunta Isgili da cewa “Tubbabe”?
AMSA : – To, wanda y ace wa wani (sabon musulunta) “Tubabbe” dominya wulakanta shi, to, shi ya kafirta.
175.
TAMBAYA : – Kamar yaro musulmi, amma bai balaga ba, sai ya musuluntar da wani. Dai dai ne?
AMSA : – Eh, dai-dai ne, domin shi ma (yaron) musulmi ne.
176.
TAMBAYA : – Ina hukuncin mutumin day a musulunta, amma bai musuluntar da iyalan shi ba?
AMSA : – To, ya gajarta, watau tilas ne mutum ya shirya da wanda ke tare da shi.
Ba ya halatta ga mutum cikin barna ka kyale shi, balle ma kafurci.
Sai ka yi kokari.l in ita kirsita ce, yana yiwuwa ka zauna da ita.
Amma in ba kirista ce, yana yiwuwa ka zauna da ita.
Amma in ba kirista ba ce (ko Bayahudiya) ce; wanna sai ka rabu da ita.
177.
TAMBAYA : – Wai ko ana iya kiran Malami; “Amirul-muminin”?
AMSA : – A’a ‘Amir’ Sarki ke nan shgaban Musulmi. Watau malanta daban, sarauta kuma daban.
Malami fada wa mutane yake yi, ga yadda ake yin (abubuwa).
Sarki kuma zartaswa yake yi.
Allah ya bambanta su.
178.
TAMBAYA : – Wannan na tambaya a kan masu kai ‘ya’yansu makarantar renon yara din nan; watau “Nursery School”.
AMSA : – To, ina fatan in dai za ku kai yara a Nursery School (Makarantar Renon Yara) din nan, ku sami matan kwarai, da mutanen kwarai su tafi su gudanar da makarantar, kada ku kai ‘y’yanku gun miyagun mutane.
Domin duk abinda yaro ya dauka (ya koya) cikin sekarunsa goma ta farko, da wuya ya bar shi har abada.
Saboda haka, wanda ya kai dan shi inda za a karkatar da shi cikin shekarar nan ta goma ta farko, to, shi kada ya yi kuka da kowa, sai da kansa.
179.
TAMBAYA : – Wai gaskiya ne,duk bayan kwana Arba’in, mutum ya aske gashin – gabansa, suuan ne?
AMSA : – Eh, sunne ne. yana cikin FIDIRAH, watau ayyukan (Sunnah) wadanda ake son yi har dai na cikon shida (6), shi ne na cire Gashin Hammata, to shi tsittsigewa ake yi, sai dai in mutum bai iya tsitsigewar, yana iya askewa. (Su ne); aske gashin baki. A tsaida Gemu da Gashin – kai, Mustahabbi ne; (sai dai ana aske gashin-kan, saboda aikin Hajji, ga namiji; da kuma Jarirai idansun kwana bakwai da haihuwa, ko namiji ko mace). Sannan kuma ga mas’habar Malik, idan Namiji ya musulunta ba a cewa ya yi aski, ammaga mas’habar dab a ta Malik ba, ana cewa idan mutum ya musulunta, zai yi aski domin ya rabu da gashin kafirci.
Sannan kuma, shi gashin-Gaba, aske shi ake yi.
KUNA IYA TURO MANA TAMBAYOYINKU KODAI TA WALL DINMU.....
#HBS SDM